This blog is created to brings for you some life stories in english language, hausa novels and latest news updates, especially on latest job in nigeria.

NPower N-Exit USSD code

 Hello everyone,here is an Npower N-Exit USSD code diaL *45665# and follow the following insruction; So 

Share:

N-power latest updates

As npower registration is on going, there are some news flowing that the portal is been hacked, disregards this information and continue with your registration, as the portal is secured. but makes sure you did not disclose your BVN details to unknown person.
some question and answers.
1. when is the registration would be close?
Answer: there is no specific closure date yet.
2. is Nteach and Nhealth only for degree holders?
Answer: No, the program are for graduates as stated early, NCE ,Diploma and degree holders who studied the related field are all qualify for the application
3. is the npower portal hacked?
Answer: NO
4. what is the genuine npower portal?
Answer: https://npower.fmhds.gov.ng
Share:

Npower 2020 registration guides

Thought the npower portal is accessible, but you're warned not to attempt the registration until 11:45pm. Adhere to the instructions meanwhile failing to do so may lead to disqualify your application.
We will post the absolute guide to be follow for easy registration.
Share:

YAR MAHAUKACIYA KASHI NA BIYU (2)

Ta daga tarin tarikicen su take tana ihun kuka tana Kiran Mahaukaciyata ina kike ? Da kyar ta dena dage dagen ta matso kusa da jaririn nan ta tsura masa ido yaron sai kuka yake tun karfinsa wani tausayinsa ya kama ta ta Mika hanu a nitse ta dauko shi ta jawo ruwan nan ta wanke masa fuskarsa ta dorashi a bayanta ta dauki zanin nan da Larai ta bata ta goya shi ta fito ta fantsama neman Mahaukaciya ,  Wai shin wacece Yar mahaukaciya? Yarmahaukaciya ita kanta bata san sunanta ba bata san na mahaifiyarta ba , ita dai ta fara wayo ta ganta a gidansu bola kuma taji yara na kiranta da *Yar Mahaukaciya* ana kiran mahaifiyarta da *Mahaukaciya* duk da irin tarin daudar da suke ciki da cin abinci marar kyau da kwana a waje marar kyau idan ka kalesu zaka gane cewar fararen mutane ne rayuwa ce kawai ta mayar da su masu duhu , Yar Mahaukaciya ba arabi bale boko , bata da kowa sai Mahaukaciya , tarbiyarta tarbiyar Allah ce domin tanada nutsuwa tana masifar son Mahaifiyarta Mahaukaciya , bata son komai ya rabeta kulun cikin shan dukanta take domin idan ta kawo mata abu mushe taki ci sai kawai ta daneta wataran ta dura mata wataran kuwa ta samu ta gudu ,
Abincinsu gida gida take bi tayi aikace aikacen ragwayen mata ta samu abinda ta samu ta kai musu su ci abinsu kuma ruwa na kwata ne kadai basa sha domin tana yin iya kokarinta don ganin mahaukaciya ta kwana da ruwa a dakin , tun tana karama suke cikin bolar nan wataran ta wayi gari taga Mahaukaciya na dauke da ciki bata san KO na waye ba hasalima sai da taji yara na fada ta gane inda suka dosa tayi mamakin inda mahaukaciya ta samu cikin nan harma tayi tunanin KO hakan kawai ake wayar gari da shi , ita dai bata da mai bata amsa hakan yasa ta yi shiru abinta take lalaba mahaifiyarta cikin tsananin so da kauna iya labarin tarihin mahaukaciya Kenan. Tafe take da dan yaro a bayanta tana girgizashi tana fadin kayi shiru dan Mahaukaciya muje mû nemo Mahaukaciyarmu mu kawota gidan mu ta goya sabon dan mu , kayi shiru Dan mahaukaciyana tana ta yawo gaba daya ta jigata sai jiri take na tsananin yunwa ga Dan mahaukaciya sai dai ta bashi ruwa yara kuwa banda tsokanarta ba abinda suke duk inda ta zaga sai an biyota ana fadin lah Yar mahaukaciya ta sato beby har ta ISO wajen wani police zata huce taji yace " ke yar mahaukaciya dan wa kika sato haka? Tayi narai narai gabanta na mugun faduwa ta ce " Mahaukaciya ta haife shi kuma ta gudu, Ya zabga mata mari har sai da ta dan fara sakin fitsari ya damketa sai police station , suna zuwa ya Nuna cewar ta sato yaro ne suka shiga tambayarta amsar dai data ce Dan Mahaukaciya ne hakan yasa suka kunce yaron suka shiga nadarta Dole sai ta fadi inda ta sato yaro banda kuka ba abinda take suna tsaka da dukanta sai ga tsohon daraja shima police din ne aman ya fisu mukami , yana zuwa ya tambayi mai tayi, Ilyasu yayi masa bayanin ai ga abinda aka kamata da shi, Tsohon daraja ya ce "tabas kwanakin baya naga Mahaukaciya da ciki a jikinta kuma yau na ganta wajen kasuwa ba cikin sanan saninta duk jini ne tabas wanan yaro *Dan Mahaukaciya ne* dan haka ku saki baiwar Allahn nan tayi tafiyarta 
Haka suka saketa ba dan ransu ya so ba domin sun so ta kwana a nan suyi anfani da ita ,sai dai kash tsoho ya kawo cikas, Da kyar take takawa domin ta daku ta dauko dan Mahaukaciyar tayi wajen kasuwar don neman Mahaukaciya tana tafe tana kuka yaron na kuka tayi kasuwa neman duniyarnan ba Wanda bata yi ba ta juyo ta nufi wani layi tana tafe 'tana kugin sunan Mahaukaciya har ta isa wata makaranta ta zauna tayi tagumi almajirai sai shigi da fici suke suna ta sha'aninsu har akayi sallar isha'i bayan an gama sallah Malan ya fito daga masalaci ya hangi yatinyar nan zaune tana ta jijiga yaro a hanunta kawai sai wani tausayinta ya kama shi ya matso yayi mata salama, Ta dago jajayan idanuwanta masy shige da na misa ta sauke su saman fuskar wanan Malan mai cike da Haiba ta amsa salamarsa 
Ya ce " Baiwar Allah lafiya kike zaune a nan? Ga yaronki da alama yunwa yakeji to ki bashi ya sha mana Yar Mahaulaciya ta kale shi tace " Malan ai ruwan ya kare babu kuma abincinsa 
Malan sai yaji tausayinta ya ce tashi mû shiga gidana a tatsa miki nonon akuya tayi sabuwar haihuwa sai ki bashi ya sha , ta mike har tana harde kafafuwanta ta bi bayansa suka shiga gidansa, Matansa biyu dayar mai kirkin gaske DAyar kuwa tadi dafi zafi hakan yasa ya nufi dakin saratu ya fada mata ta fito ta taimaki yarinyar nan da danta,Saratu ta fito suka gaisa da yar Mahaukaciya tace miko yaron a bashi nonon akuya kema kije ga ruwan dumi kiyi wanka domin da alama sabuwar haihuwace Yar Mahaukaciya ta ce " nayi wanka? Da gaske?
Saratu ta ce " eh man ga bokici ki dauka ki zuba ruwan sai ki dan sirka da na rijiyar ki je kiyi wanka shima bara nayi masa sai a bashi nonon 
Sai washe hakora take domin itadai da wayonta har ta manta rabonta da tayi wanka ta jawo isashen ruwa ta kai bayi ta aje saratu ta bata soda ta dauko mata jacen kayanta ta mika mata har tana fadin ki wanka ruwan zafin da kyau fa saboda jego ita dai har lumshe ido take tana zuba ruwa a jikinta kafin ta fito Saratu ta wanke dan mahaukaciya ta bashi nonon akuya ya sha sosai har ya samu wani ni'imtacen baci mai dadi 

Wanka take tun karfinta wani bakin ruwa na zuba daga jikinta yana bin magudadar ruwan nan da nan sai gâta ta fara haske tamtar mai , ta cire ledar dake rufe a kanta ta dauki sodar nan ta ringa kwabata a cikin gashin kanta nan da nan naga wata irin dauda mai yauki tana zuba daga kanta ta kama kwarara ruwa gaba dayanta ta darwaye jikinta dagowar da zata yi na zaro ido domin gashin kanta ba baki bane kalar 🙍🏼 masara ne yelow gaba dayansa aman yalow mai haske ga shegen tsayi da gareshi na tambayi kaina wai Yar Mahaukaciya yar hausawa ce kuwa? Ta dauko ledarta ta daure kanta ta saka kayan da Saratu ta bata sai ajiyar zuciya take domin ta rabu da kashi 80 na daudar dake jikinta tana fitowa gaban Saratu ya fadi , duk irin kirkin saratu matsalarta daya ce kishi Allah yayi mata kishin mijinta tamkar mai , hakan yasa da Sauri ta daukowa Yar Mahaukaciya yan tsumakoron da ta dadauko mata ta bata ta hada mata da tuwon lamshi mai yawa ta ce " to yar uwa rufe gidan zamu yi kinsan Malan ba a nan yake kwana ba hakan yasa Mike rufe gida da wuri  Yar Mahaukaciya ta kama godiya harda tsugunawa saratu ta ce ba komai ta dora mata dan Mahaukaciya ta goya ta dauki sauran kayan tayi gaba tana yiwa Allah godiya taci GABA da Neman Mahaukaciya..
To ya zata Kaya? Muhadu a kashi na Uku. 

Share:

shawarwari guda goma da ya kamata mace me fama da kuragen fuska tayi amfani da koda daya ko biyu daga ciki



shawarwari guda goma da ya kamata mace me fama da kuragen fuska tayi amfani da koda daya ko biyu daga ciki:

(1). Da farko ana so awa biyu ko uku kafin ki kwanta barci sai ki shafa man goge baki a fuskarki, musamman wuraren da kurajen pimples suke da yawa. kuma Ba kowane irin man goge baki za ki shafa ba, ana so ki shafa farin man goge baki ne. Idan kin ga dama za ki iya wanke fuskarki idan man goge bakin da kika shafa ya kai minti 30, idan kin ga dama kuma za ki iya kwantawa da shi har zuwa wayewar gari. Za ki rika maimata hakan har zuwa wadansu kwanaki, idan kin yi hakan za ki ga canji a fuskarki.

(2). Ki kasance mai yawan shan ruwa.yawaita shan ruwa ba wai zai sanya miki  laushin fata ba ne kawai, a’a, zai taimaka miki wajen yaki da kurajen pimples din da suke fuskarki. Haka yana da kyau ki guji yawan cin abincin gwangwani, kasancewar suna dauke da wasu sinadarai da za su rika sanya kurajen fuska. Ya kamata ki yawaita cin ‘ya’yan itatuwa da suka hada da su abarba da lemu da ayaba da kankana da sauransu.

(3). Ki rika amfani da grem irinsu (Jane Iradale) da (Neutrogenia Rapidn Clear) da (Acne Eliminating Spot Gel) da sauransu, hakan zai taimaka miki wajen daidaita man da ke fatarki, wanda masana fata suka ce idan yayi yawa yakan haifar da kurajen fuska.

(4). Ki kasance mai amfani da man (Cornmeal) a fuskarki, yakan sanya kurajen fuska su motse sannan a hankali su bace, misali man shi ne (Intagilo Clear Sal Cleanser.) Sannan ki rika amfani da man da ke hana yaduwar kwayar cutar bakteriya, irin wannan man yakan ratsa kofofin da suke fatar fuskarki da ma jikinki gaba daya, sannan yana yakar kwayoyin cutar da suke fatarki, a lokaci guda ya daidaita miki yawan man da yake fitowa daga fatarki. Zai kuma cire miki kwayoyin halittar da suka mutu a cikin fatarki. Misalinsu; (Phytomer Gommage)da Luffa-0.

(5). Yana da kyau ki ware wata rana ko wadansu ranaku a cikin mako ba tare da kin shafa kayan kwalliya a fuskarki ba, hakan zai bai wa fatar fuskarki samun‘yancin shigar da kuma fitar da iska ta kofofinta ba tare da wani cikas ba. Haka idan za ki shafa kayan kwalliyar a fuskarki, to kiyi amfani da kayan kwalliyar da basa toshe kofo fin fatar fuska.

(6) Ki kasance mai shafa mai domin fatar fuskarki ta kasance cikin danshi kasancewar wadansu kurajen fuskar sun fi bata fuska idan fuska tana bushe.

(7) Yi amfani da man (Tea Tree’) domin ba wai kawai yana baje kurajen fuska ba ne, a’a yana rage karfinsu da kuma kalarsu. Za kisami ire iren wadannan man a shagunan sayar da kayan kwalliya na zamani.

(8) Ki kasance mai yin taka tsan tsan wajen amfani da ire iren man shafawar da kike amfani da su a gashin kanki, ma’ana kada ki sake ya rika taba fuskarki hakan zai iya haifar miki da kurajen fuska, kasancewar wadansu sinadaran an yi su don su taimaka wa gashin kai ne, don haka idan suka shiga kofofin fatar fuskarki sai su haifar miki damatsala.

(9) Ki kasance mai gasa kurajen fuskarki Duk lokacin da kurajen pimples suka fito miki sai ki samu wani kyalle mai tsafta, sai ki tsoma shi a ruwan zafi, ba wanda ya tafasa ba, bayan kin tsoma sai ki fito da shi sai ki rika dora shi a kan wajen da kurajen suke, sannan ki rika gogawa a hankali, zafin kyallen yakan sa kurajen su  motse daga nan su mutu.
(10) Ki guje yin amfani da hannunki wajen fasa kurajen da suke fuskarki, domin hakan yana kara yawansu hade da sanya fuskarki ta kara cabewa.

Domin neman karin bayani a tuntubi agents namu ta whatsapp "08100806588" Haidar.
Share:

The role of extension officers and extension services in the development of agriculture in Nigeria

 If you want to download this file click here
 Domin karanta bayanan danna nan domin budewa
Share:

Npower

Npower sun fara biyan first badge daga cikin yan 2017 masu moriyar program din, tun jiya ne dai mutum dubu dari suka fara jin kuwan woyoyinsu na alert stipends nasu na watan Augusta.
Share:

HIKAYAR SHEHU JAHA KASHI NA UKU 3

DAGA ALJANNA NAKE



Wata rana Shehu Jaha ya gamu da wata mace kan hanya. Sai ta tambaye shi daga ina ya fito? Sai yace da ita daga jahannama. Da jin haka sai ta tambaye shi ko ya ga yaron ta da ya rasu a can? Sai yace da ita ya gan shi a tsaye a kofar Aljanna an hana shi shiga har sai an biya masa bashin da yake kansa. Sai matar ta bashi kudin da zasu biya wannan bashin, ta kama hanya ta tafi gida, ta bawa mijinta labarin abin da ya faru, sai nan da nan mijin nata ya zabura ya hau dokinsa don ya kamo barawon. Ko da shehu ya hango shi, sai yayi wuf ya fada wani gida da ake yin nika, yace da mai nika, don Allah ka cece ni wani Azzalumi ne ya biyo ni, saboda haka taimakon da zaka kayi mini shine ka karbi rigata ka sanya, ni kuma ka bani taka na sa, sai ka hau wannan bishiyar ka buya a cikin rassanta. Sai mai nika ya amince da wannan bukata, da mai gida ya iso gidan nika ya shiga, ya tambayi inda barawon yake, sai shehu ya nuna masa mutumin da yake kan bishiya, nan da nan sai mutumin ya cire GWADONSA ya bar dokin sa, ya hau bishiya don ya kama barawon, sai fa Shehu ya dauki gwadon ya yi maza ya dare dokin ya sheka a guje. Bayan nan sai mai doki ya dawo gida a kasa, ya ce da matarsa babu shakka mutumin nan daga lahira yake kuma can zai koma, saboda haka na ba shi mayafina da dokina na ce ya hada da kudin da kika ba shi ya kai wa yaron...hahahhhahah
Share:

HIKIYAR SHEHU JAHA KASHI NA BIYU 2



shehu yayi aure, sai abokansa suka shirya masa walima, to daga cikin abincin da aka shirya akwai waina mai rai da lapiya, amma da suka zo cin abincin sai suka manta basu kirashi ba, har suka cinye wainar. shi kuwa ya kasance mai son waina kwarai da gaske. saboda haka sai ya cika da fushi. daga baya suka nemeshi basu same shi ba ba. sai can suka same shi tare da wani dan uwansa, suka taho dashi, da yazo sai abokan nasa suka ce dashi: yaya ana bikin ka kuma kayi tafiyar ka naka guri? sai yace ai bana bukatar auren, ku aura wa wanda yaci waina. hahhahahaah 
Share:

HIKAYOYIN SHEHU JAHA KASHI DAYA 1




AI SAI NA ZAMA SHASHA HAWA BIYU

Wata rana shehu ya tafi ya kai alkamarsa wajen nika, da ya isa gurin sai ya rika diban tafi dai dai daga buhunnan mutane yana zubawa a buhunsa. Sai mai nika yace: lafiya kuwa, mene ne haka? Sai yace kai ni fa shashasha ne, duk abin da hankalina ya shirya mini shi nakeyi. Sai mai nika yace: to, idan kai shsha ne me yas baka debo alkama daga buhunka ka zuba a buhunnan mutane? Sai yace : ai ni shashacina mai sauki ne, idan kuwa na aikata abin da ka fada, sai na zama shashasha hawa biyu..

Share:

*'YAR MAHAUKACIYA KASHI NA DAYA 1




Ko karin amai take tana jan nunfashinta , ita kuwa ta daneta ta matse mata baki ala Dole sai ta dura mata danyen misan da ta tsinto a cikin bola , MAhaukaciya ce na hango ta dane wata yar budurwa tana kokarin dura mata mushe a bakinta ita kuwa ta gumtse bakin taki budewa , tana tsaka da kokowa da ita sai naga ta dakata , ta ja da baya kuma sai naga ta saka ihu ta shiga shure shure tana dafa cikinta da alama nakuda ce ta taso mata , yarinyar nan naga ta taso da gudu tana ta bibiyar wanan mahaukaciyar tana fadin , sanu haihuwar ce ?

Ita dai Mahaukaciya ba bakin magana banda juya kai ba abinda take hakan yasa yarinyarnan fita da gudu daga cikin tsumakoran da suka saka suka dadaure sukayi dan dakinsu inda zapi , sanyi , damana ke riskarsu , tana FIta tayi ta gudu tana haki da kyar ta samu ta fito cikin layin domin a can cikin bola ne suke can karshen anguwa , tana fitowa ta tsaya tana waige waige ta rasa ina zata dosa domin neman taimako , wani gida ta hango tamkar kango ta nufa domin wani lokacin sunkan sakata kai shara gidansu wato bola , su bata dan kanzo da ruwan daurayarsu na kayan wankin su wani lokacin har barinta suke ta debi na rijiya taje su sha dadinsu ita da Mahaukaciya ,

Tana shiga ta rafka salama ta ja gefe ta rakube , wasu yara naga sun fito su kansu daudar jikinsu ta ishe su suna ta wasa suna ganin wanan yar budurwar saï naji sun fara wake suna fadin *Ke mai suna Yar Mahaukaciya yaya haukan ki Yar Mahaukaciya , shin ina babarki Mahaukaciya tana ta zuba haukan? Yar mahaukaciya* ita kuwa sai murmushi take aika musu bata ce komai ba , har suka gama daukar maganar su suka tafi abinsu , ta kusan rabin awa a tsaye sai ga uwar gidan ta fito ta sha damara da niyar yin surfe tana ganin Yar mahaukaciya tayi hamdallah ta yafitota, Yar mahaukaciya ta matsa da Sauri ta zuguna a gabanta ,
Larai ta ce " idan abinci kike so zan baki da ruwan rijiya ke harma da zanin daurawata aman sai kin surfe min wanman dawar gaba dayanta, Yar mahaukaciya ta juya inda aka nuna mata dawa ta hadiyi wani yawu mai daci ta ce " To uwar gida ran gida zan surfa yanzu kuwa?

Larai ta washe hakora ta kama mata buhun dawar suka tsayar da tirmin da tabaryar ta gyara yagegen zanin dake daure a jikinta ta shiga daka ba kakautawa , tun da rana ba ita ta gama ba sai yama lilis , Larai ta aiketa tayo mata cefane taje har cikin kasuwa a kafarta ita dai fama take ta gama ta koma wajen Mahaukaciya tasan yanzu ta dena iface ifacen domin takanyi hakan ,
Ba ita ta gama bautar gidan yawa ba sai da wajen shigar magariba , larai ta harhado mata abinci harda na shekaran jiya ya gama yin tsami ta turo mata harda kanzo ta sauye mata shi a cikin wani bokici da ya gama yin tsatsa sanan ta ce ta jawo guga biyu ta isa gudun kar ruwan rijiyar ya kare ta je ta jawo guga biyun ta sauye a tsohuwar jarkarta ta dauka gaba daya tana tafe tana Sauri yara kuwa sai binta suke suna fadin yar Mahaukaciya ita kuwa bata kulasu famarta ta isa bola Tana zuwa ta hango dan karton da ta kara ta rufe an janye shi ta kara Sauri ta shige cikin kewayen nasu , jini jini ta fara gani a dashe a ko'ina ta yaye rufar da tayi da ledodi tana yayewa gabanta na faduwa don abinda idanuwanta suka gani bata san sanda ta saki bokicin abincin da ta wuni tana aiki dalilinsa ya zube a nan ba ta dauki hanunta ta dora saman kanta saman bakar ledar da tayi dan kwali da ita ta kurma ihu domin jariri ta gani konce cikin jini yashe a nan gashi ba Mahaukaciya ba alamarta da gudu ta karasa ta shiga dage dage da alama neman Mahaukaciyar take.
 Shin ina mahaukaciya? Yaron nan wa ya haife shi? Su waye Mahaukaciya da Yar Mahaukaciya? mu hadu a kashi na biyu.


Share:

ALJANAR FATIMA KASHI NA BIYU




kujerar da yake zaune.  Fararen kaya ne a jikinta amma gaba daya sun baci da jini wuyanta a yanke jini na zuba har tsartuwa yake yi. Idanunta kuwa sunyi jawur jini na bulbula daga ciki haka hakuranta sun kara zarowa sun fito waje jini cike da bakin.  Kuma a hakan murmushi take wani irin sauti na fita kadan-kadan.............
😰 Kodai aljana ya zane 🙆🏻??
Muktar da gaba daya ya tsorace ya gigice har ya fadi. A hankali ya dago kai dan kara tabbatar da abunda ya gani shin ko gaskiya ne ko kuwa idanunsa ne kawai suka nuna mishi hakan.  Abun mamaki a dagowar da yayi wayam yaga gurin ba komai. Yana nan dai a tsaye yana tunane-tunane wannan al'amari domin yasha kai karfe sha biyu amma tun da yake yau kusan shekara daya da bude shagon amma ba'a taba tsorata shi ba sai yau "shin ko dai da gaske gamo nayi" ya tambaya kansa. 

Karar da ta doki dodan kunnan sa ne ya dawo dashi daga tunanin da yake.  Daga bangaren hannunsa na dama karar Kofatu kamar duban dawaki  ne suka nufo shi yaji.  Nan da nan ya juya a firgice yana neman fadawa shago.  Wasu bakaken hallitu ne wanda masu jikin doki dukan su bakake ne amma ba kai a jikinsu sune suka nufo shi a sukwane.
Koda idanunsa sukayi tozali da wannan mugun abu, hankalinsa ne ya dugunzuma dan tsabar tsorata a million ya fada shago bai ko tsaya kulle shagon ba haka kuma baisan lokacin da ya tsallake dogon bincin da ke raba masu sayayya da cikin shagon ba. A bayan bencin ya sama wani dan lungu ya labe yana maida nunfashi day-day. Duk jikinsa karkarwa yake idanunsa nan-da-nan suka saki ruwa.  Kuka ya farayi shabe-shabe ya fara magana a hankali cikin muryar sa dake rawa yana fadin "Wannan wane irin bala'i ne ni kam yau na shiga uku..."  Surutai ya tayi shi kadai sai da ya dau kusan mintuna 20 a cikin shago yayi lumi ko motsin kirki baya yi kuma karar dawakin nan har yanzu a kwaita.
Can dai yaga wannan bata yi ga zafin dake adabarsa sai gumi yake, hakan tasa shi fitowa daga inda ya labe a hankali ya dan leka kofar shagonsa wayan baiga komai ba sai karar da yake ji. Ya dade nan a tsaye ko zaiji karar ya ragu amma ba alamar raguwar. Ga zafin ya fara cin karfinsa ya fara magana cikin murya irin ta mai kuka ko gunguni. "Haba wllh fita zanyi bazan tsaya zafi ya kashe ni a banza ba. Wallahi fati zanyi ko me zai faru ya faru. Juyawa yayi ya dauki makulan shagon bai ko tsaya debe kudinsa ba. Ya fara yunkurin tsallakowa  bayan ya tsallako ne ya bi a hankali kamar munahiki ya leko shagon ta bangaren da yake jin karar. 
Leka warsa keda wuya sai yaji kamar an dauke wuta dif! Karar ta dauke. Hakan ya bashi dama da karfin gwiwa na fitowa da sauri ya garkame kofar shagon yanufi hanyar gida da gudu-gudu sauri-sauri takun da yayi bai wuce 15 ba sai gani yayi wutacen nan gaba daya sun dauke dif!. Al'amarin da tasa shi yayi tsaye cik kenan. Kamar walkiya haka yaga wani farin abu ya gifta ta gaban shi duk da duhun amma yaga abun kamar mutun lokacin tsoro ya kara rufe shi, Suman tsaye yayi a gurin tsabar tsorata da yayi.  
Sanda aka shafe kusan mintuna 10 yana wajen a tsaye ya rufe idanu alamun haske ya gani hakan yasa ya bude idanunsa ai kuwa sai yaga wutar ta dawo. Nan fa ya ranci ta kare ya zura a guje kamar wanda zai tashi sama.   Yana wuce wani mangwaro yajiyo dariya a saman shi, a cikin gudun ya wai-wayo abunda ya gani ne yasa shi har saida yayi tuntube karfin gudun yasa har sai da ya wuntsila yayi kungun bala.  Yarinyar nan ya gani kamar dazun duj jini na fita a jikinta kuma itace ta dage kai sama tana gagaba dariya marar dadin ji.
Bai kula da ko yaji ciwo ko baiji ba. Ya tashi ya ruga a guje yana ihu.  Bai daina ganin yarinyar na fito mishi a sifofi na ban tsoro ba har ya kawo gida. Da shigar sa gida ko tsayawa sa kubobin kawai banka kofar yayi. Dake yasan kyauran mai jamlock ne.
Da gudu ya fada daki UⓂⓂEIY ZEEY (matarsa) na kwance a kan gado tana barci. Yabi ta kanta ya tsallaka dayan gefan tuni ya ja (blanket) bargo ya rufa duk zafin da ake fama da shi. Nauyin sa ne ya tayar da  Ummiey daga barci waigawa tayi dan ganin waye sai ganin shi tayi ya kudun-dune cikin bargo yana sauke nunfashi day-day tayi mamaki mutumin da baya san zafi ko kadan kullum in yazo sai ya mayar da fanka ta bangaransa amma yau gashi ya shiga bargo lalai ba lafiya ba.
"Mai gida-Mai gida baban HAWWER-baban HAWWER lafiya kuwa?"  Haka ta dinga jero mishi tagwayen sunaye hade da dadabarsa tana tambayarsa. Karkarwa taga duk jikinsa ya hau yi.  Domin shi kam abunda yake ji yayin da yake ji bashi take fada ba kuma ba muryarta yake ji ba.  Domin wata murya yake ji mai abun tsoro tana fadin "Mu...ktar...m..u..ktra" a slow muryar ke tafiya. 
 Ummiey ganin karkarwar da yake tayi yawa ta dan daga murya "Baban Hawwer lafiya kuwa".  Yayin da shi kuma yaji an daga mishi tsawa da wata muryar mai razanarwa ance, "Kai muktar magana fa nake maka".   Firgigit ya tashi zaune. Maimakon yaga matarshi ummiey. Yariyar nan ya gani kamar yanda take dazun dan yanzu ma tafi ban tsoro domin dogon gashin kanta mai-makon ya zuba a bayanta sai mikewa yayi tsaye cir! Yayi wani irin fadi A sama. ('Kai duk wanda yayi arba da wannan yarinya ala dole hantar cikinsa ta kada dan tsoro, In ma bai sume ba')
 Muktar kuka ya farayi yana ja da baya-baya yana bata hakuri a haka har ya surmuyo kasa daga kan gado bai ko jira kuma ba yaci gaba da ja bayan.  Ummiey na gannin mai gidan nata ya fado daga kan gado yana kuma kallonta yana kuka ta tabbatar da ba'a hayyacinsa yake ba. Hakan yasa ta matso daga kan gadon ta sakko a hankali take binshi tana tambaya. "Baban hawwer wai me ke damunka ne?, ka min magana mana". 


Yayin da shi kuwa yarinyar yake gani tana tunkaro shi hakan yasa ya kara sauri wajen jan gindin da yake yana yin baya yana fadin.  "Na shiga uku yau naga ta kaina, dan allah kiyi hakuri karki kashe ni shin dan naki taimaka miki shikenan nayi laifin da za'a azftar dani har haka. *DAGA TAIMAKO*   dan allah karki kashe ni".
Ummiey da jin wannan kalamai na fita a bakin mijin nata sai tayi tsaye cik! Tana kallon shi cike da mamaki tana cewa "Lalai baban hawwer yau ba lafiya kake ba. Yanzu ni din kake cewa zan kashe ka ni?".
Yayin da shi kuma yake jin wani abun daban sabanin abunda take fada.  Domin shi yarinyar yaga ta tsaya tana gagaba dariya kafin ta fada da murya mai fitowa bibiyu. "Kai muktar ka sani ka debo ruwan dafa kanka, a cikin kifayen da kake kamowa yau ka kamo ajalin ka. Nan take yaga wata wulshe-shiyar wuka ta bayyana a hannun yarinyar.

Ihu! Ya fara kurmawa yana fadin "Wallahi na tuba baran kara ba, dan allah ki yafe min duk abunda kike so zan baki. Duk lokacin da kikaji yunwa ki dinga zuwa ina baki abinci ko da kuwa zakiyi ci Goma ne a rana amma dan allah ki taimaka kiyi min rai karki kashe ni".  Ummiey taga abun da mijin nata yake ya fara yawa harda ihu nan ta fara tunanin ko ta leka ta kirawo makwabcin su ne. Kuma sai dai tace bari ta karasa gare shi.  Tahowa tayi cikin sauri ta mika hannunta zata taba shi. Ihuu! Ya kurma mai razanar wa kafin ya zube kasa sumame. domin shi yarinyar ya gani ta zo kanshi ta daga wuka zata caka mishi................
Tahowa tayi cikin sauri ta mika hannunta zata taba shi. Ihuu! Ya kurma mai razanar wa kafin ya zube kasa sumame. domin shi yarinyar ya gani ta zo kanshi ta daga wuka zata caka mishi»   Ummiey gaba daya ta firgice kamar ta kurma ihu! Itama.  Ganin mai gidan nan nata a kass sumame. A rude tayi waje tana zubda hawaye. Da sauri taje ta bude randar kasar ta wacce ruwan ciki yayi sanyi sosai kamar ansa kankara tasa moda ta kwalfo tayi cikin daki da gudu.
Tana zuwa batayi Wata-Wata ba ta kwaraya mishi gaba dayan ruwan da ta debo. Firgi-git ya mike zaune yana nishi yana yan waige-waige kamar wanda yake neman wani abu  dayan hannun sa kuma goge fuskarsa yake domin ruwanda Ummiey ta kwaraya mishi. Ganin baiga abun da yake zatan gani ba yayi saurin mikewa ya nufi kofar daki a guje ya rufe ya sakala kubobi biyu yana fadin.
"Ummiey wllh kashe ni zatayi taimaka ki kama a jawo wardrobe  din nan a kara rufe dakin".  Ummiey kam tsaye tayi ta saki baki tana kallansa yanda duk yabi ya rikice yake abu kamar mahaukaci.  "Baban hawwer wai  lafiyar ka kalau kuwa? Ya kake wasu irin abubuwa ne haka wanda ban taba ganin kayi kwatan-kwacin kalar su ba?". 
Tsawa ya daka mata kamar yanda ya saba dama baya jiya mata dadi, ba dan Ummiey mai hakuri ce ba da tuni ta bar masa gidansa to amma sai akaci sa'a irin matan nan ne masu hakuri tayo gadon gidansu dake babban ta shine limamin masalacin juma'ar anguwar kuma baban malammi ne masani.  Itama kuma haka tayi sauka har biyu.
Zabura tayi tsawar da ya daka mata.  "Nace miki kizo ki kama wannan wardrobe din mu kai mu rufe kofar aljana ce in ta sake shigowa kashe ni zatayi".
Ummiey sai yanzu ta gane mijin nata gamo yayi. "Baban hawwer wacce aljana kuma"?.  "Oh! My god ya fada. Tunda bazaki kama min ba baza ki taimakawa mijinki ba so kike ta halaka ni to bari in kai ni ai zan iya". Kiki-kiki ya jawo wardrobe har kofar dakin ya danne kofar. Danne wa keda wuya yaji an fara girgiza kofar dakin da gudu ya haye gado ya lulube. Ummiey ce tazo kanshi ta fara tofa mishi addu'o'i har allah ya taimaka barci yayi gaba da shi. 
Tunda asuba da ya tashi yaci gaba da zabur-zaburansa. Ummie na tofa mishi addu'a amma taga abun yafi karfita hakan yasa ta dauki waya ta kira babanta tana kuka ta gaya mishi duk abunda ya faru. Yace gashi nan zuwa. Mukhtar ba abunda yake  sai surutai duk bayan yan mintuna kuma sai ya dinga tsorata yana boyewa yana fadar "gata nan gata nan".!   Ummiey ita kanta ta shiga rudani.
Ba'afi mintuna 20 ba malam hamza ya karaso gidan koda Mukhtar ya jiyo sallamarsa da gudu ya fito ya makal-kale malam yana surutai saida malam yayi da gaske tukun ya raba jiknsa da na Mukhtar lokacin ya fara tofa mishi adduo'i tukun ya samu haukan da yake ya dan lafa malam yasa shi ya zauna a tabarma da ummie ta shimfida. Bayan sun zauna ne malam ya fara karanta ayyatul kursiyyu tare da sauran ayoyi masu karfi.  Ba'a dade da fara karatun ba sai ganin wannan yarinyar ta bayyana cikin kayan da Khadija ta saka mata.  A gaban malam ta zauna hade da musu sallama. Muktar har zai ruga malam ya zaunar da shi. Hatta ummie ta tsorata domin ganin abun tayi kamar a mafarki.
Malam ya kalle ta yace "baiwar allah me wannan mutumin ya miki an bani labarin irin azabtar da shi da kika yi jiya". Muryar ta ba dadin ji tace, "ka tambaye shi malam shi ai yasan abunda yayi".  Malam baiyi gardama ba ya juya ga muktar ya tambaye shi me ya mata. "A tsorace yac malam wallahi ba abunda nayi mata shagona taje tana nuna alamun yunwa take ji a rana ta farko na kore ta a rana ta biyu kuma ganin ta takura min na dake ta".
"Karya kake muna fiki azzalumi macuci, Ko daya ba dan wannan ne na shiga rayuwarka ba. Wannan ma nayi ne dan in tabbatar da rashin mutuncin ka da mutane ke fada sai naji kai da bakin ka ma fada kake. Malam muktar Shin har ka manta abunda kayi shekara daya da rabi baya da suka wuce?.  Yarinyar ta fada cikin tsiwa tana hararen shi. Nan fa kwakwalwarshi ta shiga juya mai yana kokarin tuno wani abu.  Ganin ya shiga dogon tunani ta sake daga mishi wani tsawan wanda ita kanta ummie ta firgita kamar ta fada daki taji.  "Kaaaai!  Mugu wato har ka manta yaron da ka kashe ka rabasu da dukiyarsu ka raba yaya da kanwa. a fadama ko?".   Dummm!  Gaban muktar ya fadi jin ta tado zancen da a tunaninsa ba wanda ya san shi daga allah sai shi sai kuma wannan yarinyar.  (What!) "Yaron da ya kashe?".  Ummiey da malam ne suka fadi hakan a tare.
Bugun kirjinsa ne ya tsananta nan take jikinsa ya fara bari. Motsowa ya farayi gaban Yarinyar yana fadar "Dama ke aljana ce ban sani ba. Don allah ki rufa min asiri karki tona wannan sirrin duk abunda kike so  zanyi amma ki taimake ni karki tona wannan sirrin...."  Tsawar da ta daka mishi ce ta tsayar da shi nan take ta wani bata rai fuska ba wal-wala. "Bani bace domin dani ce da bazaka kwana ba a ranar. Ka basu labarin abunda ka aikata wa wannan yarinyar da kanka, in kuwa ba haka ba yanzu ka gayawa yan garin ku". Ta karashe maganar cikin daga murya. Nan take tsoran Mukhtar ya karu. "To-to bari in fada amma dan allah karki min komai". 
Malam da diyarsa ba abunda suke sai kallo da sauraren ikon allah. Ummiey tunani take shin wannan wane BOYAYYEN AL'AMARI ne? Wanda bata sani ba game da mijinta. Ita dai bayan mugun halin sa da kowa yasan da shi bata kuma san da wani ba. Mukhtar ganin kowa yayi shiru shi ake saurare ga kuma wannan aljanar da ke mishi wani mugun kallo mai tsoratarwa. Ya shiga basu labari..............................

 MU HADU A KASHI NA GABA....

Share:

ALJANAR FATIMA KASHI NA DAYA



A Cikin kado anguwar hausawa dake babban birnin tarayya Abuja.anguwa ce mai lunguna gata da tarin bishiyoyin  mangorori hankan ne yasa anguwar take da inuwoyi hakan ta haifar wa da wajen duhu dan daga ance ma karfe 6 tayi to sai an haska fitila tsabar duhu in dai ba farin wata ba. Anguwa ce  mai tarin jama'a, ko ta ina ka duba mutane ne kowa na uzurinsa. Akwai masu saide-saide da yan shaguna da irin tsofafin nan masu saida kayan makulace na yara.
              Wata yarinya ce sanye da doguwar farar riga wacce ta koma baka dan tsabar datti, Yarinyar fara ce kallo daya zakayi mata ka gane hakan saidai dauda ta masheta baka.  Gashin kanta mai tsayo ne amma rashin gyara yasa duk ya fara cicirewa tsabar datti gashi duk ya barbaje mata a fuska sai ta dage shi tukun take iya ganin gabanta. 

Duk mai tausayi yaga yarinya to dole tausayinsa ya lunku a kanta. Domin tayi kalar ban tausan.  A hanakali take tafiya har ta isa bakin kofar wani shagon saide-saide.  Bakin kofar shagon taje tayi tsaye ta dan yace gashin da ya lilube mata fuska tana kallan cikin shagon. Shi kuwa mai shagon a lokacin ya dan duka daukar wani abu.  'Da dagowar shi duka hada ido da ita sai ji yayi gabansa yayi mugun faduwa.

 Nana take yanayinsa ya canza kalo daya zaka mishi ka gane ya fusata ainun!, "Ke uban me zan baki iyee?, haka jiya ma kika zo kika min tsaye a kofar shago kina wani nuna min ciki da baki, gaki yau kin kuma Dawowo uban me zan miki".
  
Dayan hannuta ta daga ta dage baki hade da nuna yatsar ta cikin bakin tukun ta sauke shi ta nuna cikin ta kamar dai yanda tayi mishi jiya. Wanda duk me hankali in ya gani zai gane tana nufin yunwa take ji tana bukatar abinci,  Shima kuma kanshi ya fahimci hakan.

"Kaji rainin wayo ah! Lalai wannan baki sanni bane baki san bani da mutun ci ba to wllh yau zan nuna miki, to ni ubanki ne da zaki ringa nuna min kina jin yunwa ko dan kinga jiya korar ki kawai nayi ban taba lafiyar jikin ki ba.  Bari ki gani".
Nan take ya juya ya dauko dorina mai baki biyu wacce take jike dai mai dan tayi zafi yasa ta a mankyada Dama saboda yara ya saye ta. Goge bulalar ya fara yi domin abun man har yanzu akwai maski duk abun nan da yake yi yake yana surutai. Wato baki san na dade banyi zalinci ba ko ni dama zalinci ai rigata ce in banyi shi ba ji nake kamar a zigidir nake".  Juyowa yayi a zatansa tuni taji tsoro ta gudu ganin ya dauko bulala, amma sai yaga sabanin haka ta sake bude baki ta nuna mishi kamar yanda tayi dazun.

Kara fusata yayi da sauri ya bude yar karamar kofar ta kata ko ya fito. Baiyi wata-wata ba ya fara tsula mata bulala harda riketa yana fadin, "Bari in zane ki tukun gobe ma ai sai ki dawo kaji jarababiyar yarinya ni da ba ubanki ba taya zan baki abinci" yana yi ne yana dukanta tun tana kuka a hankali har ta fara ihu! Abunda da ya jawo hankalin mutane makwabtan shagon sa kenan. Sukayo mishi can  aka kwaci yarinyar shi kuwa sai masifa yake.  Wai ta rainashi gobe ma ta dawo.
  
Wani dan saurayi ne naga ya kama Yarinyar yana lalashita bai ko ji kyamar ta ba kamar yanda sauran mutanan gurin sukayi.  "Yi shiru yi hakuri yarinya kinji. Haba muktar yanzu dama rashin mutuncin naka har ya kai ga haka  ban sani ba?, Ai da na dauka rashin mutuncin ka da masifar bai wuce iya manya ba ashe hada yara". A cewar wanda ya kama yarinyar yana lalashi.

"Eh kamalu da ba ka sani ba kuma da ji kake yi yanzu kuma gashi ka gani da idanunka iyhee! Nayi rashin mutuncin in da yanda za'ayi dani ai sai ayi mugani".
Da jin haka mutanan wajen suka watse suka barsu su biyu a gun domin kowa gudu yake ya wa Muktar magana ya mai rashin kunya, Dama a wajen kamala ne kadai baya raga mishi duk rashin mutuncin shi yana tsoran kamala.

"Kadai kaji kunya wallahi, yanzu wannan karamar yarinyar me tayi maka da ka dake ta?".
Muktar ya wani taso da masifa kamar zai haiye kamal din, " Kai kamala ka bar ganin fa ina daga maka kafa wllh ba tsoranka nake ji ba, ya za'a yi kazo kana min maganganun banza a kan wata yarinya wacce gata nan dai kamar ma yar mahaukaciya domin wannan tafi karfin ace mata ma almajira, kawai tazo kofar shagona tana daga min baki wai yunwa jiya na koreta yauma shine ta dawo shiyasa zan zane ta gobe ma in ta dawo haka sai na zane ta". Yana gama fadar haka bai ko tsaya sauraren kamal ba ya juya ya shiga shagon shi.
Kamal jin saboda ta nema abinci ne ya dake ta dan takaici bai sake cewa komai ba ya kama hannun yarinyar ya nufi gidansa da ita dake ba nisa daga nan. Yana rike da hannuntq tana binshi suka shiga gidan, matarsa Khadija tana shara a tsakar gida tana jin salamar shi ta mike tsaye tana kalanshi tana kuma kalan yarinyar.

"Baby sannu da zuwa wannan fa daga ina". ta fada lokacin da take kokarin kama hannun yarinyar. Kamar rai a bace ya kwashe duk yanda akayi ya gayawa matarsa, khadija nada mutunci sosai nan take taji tausayin yarinyar da sonta a cikin ranta.  Gogewa yarinyar hawaye tayi hade da cewa, "Yi hakuri kinji yan mata share hawayen ya sunanki daga ina kike".  Wannan tagwayen tambayoyin ta jera mata, amma shiru yarinyar batayi magana ba sai ido da take binsu da shi.

Kamal ya maimata tambayar kamar yanda matar tashi tayi amma shiru. Sun tambaye ta ya kai sau biyar amma ko umh! Bata ce ba sai idanu da take binsu da shi. "Baby inaga fa wannan yarinya kurma ce shi yasa ma bataw Muktar magana ba".
"Kwarai nima nayi tunanin haka,  yanzu abunda za'ayi ki taimaka ki mata wanka ki zuba mata abinci taci bari inje in sayo mata wata rigar ji kafarta ko takalmi babu bari in hado da shi".  A cewar kamal domin yasan matarsa ba mai bijirewa umarninsa bane ko  mi ya gindaya mata inda ba na sabawa allah bane tana iyakar kokarinta.

"To baby a dawo lafiya". ta fada lokacin da ta mike shima kuma ya fita Kafin wani dan lokaci tuni khadija tayi wa yarinyar wanka ta wanke mata kai. Tsabar dauda saida ta bata kusan bokiti uku da mai tsantsami ce bazata iya ba domin ko ita tanayi tana dode hanci dan tsabar wari.  Bayan ta gama wankan bata mayar mata da rigar ba wani zaninta ta dauko ta liliba mata tukun ta shigar da ita ta zuba mata abinci. Ita kuma kamar wanda ya shekara baici ba haka ta fara ci hannu baka hannu kwarya. Tana gama cin abincin sai ga kamala ya shigo da sabuwar riga da takalmi mai kyau. Ya kawo ya mikawa khadija yace "ki saka mata ni zan koma shago karki bari ta fita waje". 

To khadija ta ambata. Kamala ya kalli Yarinyar mamaki ne ya cika sa ganin irin kyawan da ke gare ta ashe dama tsabar datti ne. Baidai ce komai ba ya juya ya wuce.
Khadija ta shafawa yarinyar mai mai kanshi tukun tasa mata kaya. Ta kuma tatara gashin kanta wuri guda tasa ribbon dinta ta daure mata kan, ta jawo ledar ta bude taga ashe doguwar riga ce mai wando harda dan gyale. Ta saka mata tukun ta mikar da ita tsaye ta tsaya ta kare mata kallo sama da kasa. Wow× Masha allah beautiful baby kenan,   yarinya da shegen kyau kamar aljana.

 (Nasmat tace, kaji min mata me ya kawo maganar aljana kuma a nan ko dai so kike ki tunawa king) Khadija tace "bari in saka miki jan baki da hoda kina so".  Lokacin tama manta da yarinyar bata magana. Bisa mamaki sai taga Yarinyar na girgiza kai alamun eh. Dan dariya taye hade da cewa "dama kina jin  magna ne bakya yi".  

Nan ma girgiza kai tayi alamun eh, Nan fa murna da farin ciki ya cika ta. Ta kuwa fara jero mata tambayoyi kala-kala.

'Acikin tambayoyin ne ta tambayi ina ne gidan su ta nuna bata sani ba ta sake tambaya ina iyayanki nama ta nuna bata sani ba har da hawaye. Khadija ta shiga lalashi tace "daga yau na zama maman ki kin yarda". Girgiza kai tayi alamun eh Nan take khadija ta rungume ta cikin farin ciki domin allah ya zuba mata san yara kuma har yanzu allah bai bata haihuwa ba sau biyu ko ta sama cikin bari take.
 (😭 ayya allah sarki allah ka bawa duk mai irin wannan matsala haihuwa sister na allah ya kawo 👏🏽) Haka dai ranar Khadija ta wuni cikin farin ciki duk ina tayi yarinyar na biye da ita tuni suka yi sabo har da wasanni a tsakanin su.   Da magariba haka kamala ya dawo ya tarar da su khadija ta bashi labarin duk abunda ya faru ta gaya mishi ashe tana ji magana ce bata yi. 

Nana shima yayi mata mgana ta gyada kai. Kamala yace "To yanzu bata magana taya zamu san sunanta?". 

Khadijah tace "kaji wata matsalar kuma ni nama manta in tambaye ta tun dazun. (Ta juya wajen ta) kin iya rubutu".  Yarinyar ta girgiza kai alamun a'a. Kamala yace "to mu saka mata suna waleeda mana tunda dai can dama muna san sunan".

Khadija tayi murmushin jindadi ta kalle ta tace,"Kin yarda sunanki waleeda?". Da sauri ta girgiza kai alamun eh tana dariya nan fararen hakoranta suka bayyana. 
  
Bayyan isha'i sunci abinci sun suka danyi kallo kadan wajen karfe goma suka tashi ita kam yarinyar tuni tayi barci ma. Khadija ta dauke ta suka nufi daki suka kwanta a tskiya suka sakata khadija saida ta kare wa yarinyar kallo da kyau tayi murmushi tayi mata kiss haka shima kamala san yarinyar ya shiga zuciyar su lokaci guda.

Khadija saida ta dora wa yarinyar hannu ta dan rungume ta tukun ta fara barci.

Uhmmmmm wannan kenan😊
Misali  karfe 11:00pm   anguwar nan shiru kake ji ba motsin mutane sai kukan tsuntsaye na saman mangwaro. Badan fitulun sola da suka haske anguwar ba da duk jarumtar ka bazaka iya bi ka wuce ta cikin wannan layin ba.

Shaguna duk a kulle sai shago daya wato na Muktar shi kadai ne a bude inda sabo an saba kowa ya watse a barshi shi kadai a gurin domin sai yayi lissafi tukun yake tashi.  Zaune yake yana kirga cinikin da yayi yana washe baki domin yau anyi ciniki sosai a shago. Ta wutsiyar ido ya hangi kamar wani bakin abu na tafiya a kan hanya zai gifta ta kofar shagon shi.  Da sauri ya dago kai dan ganin miye amma wayam. 

Komawa yayi yaci gaba da lissafin sa ba'afi seconds 30  ba ya kuma ganin wani jan abun kamar mutu kuma ya nufo shagon sa.  Da sauri ya sake dago kai a karo na biyu  nan ma baiga komai ba. Mamaki ne ya cika shi a fili yace "Kai miye haka kuma?".  Ajiye kudin yayi ya fita waje a sauri ya wa-waiga ko ina har saman bishiyoyin wajan amma shiru baiga komai ba.  Hakan tasa yace a zuciya "Ba komai kawai tsorata kaina ne nayi ashe".   Juyowar da yayi da niyar ya koma shago yayi tozali da abunda yasa ya kwada ihu! Hade da faduwa dan razana. 

MU HADU A KASHI NA BIYU............
Share:

DO MIN SAMUN IN GATTACCEN WEBSITE DANNA NAN


ciga nan domin wosu muhimman bayanai

Wikipedia

Search results

Popular Posts

Total Pageviews

Followers

choose your language

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *