This blog is created to brings for you some life stories in english language, hausa novels and latest news updates, especially on latest job in nigeria.

MATAR DR. SAIYADEE KASHI NA DAYA

                               

Kwance take kan gado tayi ruf dah ciki idanta biyu Amman tah rufe su tamkar mai bacci, daga ganintah kasan tanah cikin damuwa dah alamun tayi kuka tayi nak, Oh ni Ummulkhair Allah kazaba min mafi alkhairi arayuwa abinda naji tah fad'i kenan, sallah taji ana kira tamik'e taje tayi alwala tayi sallah bayan tah idar neh tah mik'a hannu kan gado tah dauki wayantah dubawa tayi taga Sam babu missed call dinshi koh daya, jiki asanyaye tashiga dailing numban sa, saida takira sau hudu har tah fidda rai sannan yadauka,
Salam'alaikum,
Wa alaiki salam Ummunah, ya kike?
Lafiya kalau Alhdulillahi ya aiki,
Aiki dah godiya Ummunah gashinan munata fama ai,
Sannu Allah yataimaka kace za.......
Inazuwa inazuwa Ummunah zankira ki aikinakeyi,
Baiko bari tak'arasa magana bah sai Jitayi phone d'in yayi cutting gabad'aya jikinta yayi sanyi kwanciya tayi kan daddumar tanah kala~kalan tunani har bacci yayi awon gaba dah itah,

  Wacece Ummulkhair?
Ummulkhair d'iya Ce ga Alhaji Abu Sufyan dah Hajiya Hadiza, Su biyu neh kadai awajan Iyayen su daga itah sai K'anin tah Affan, Ummulkhair doguwa Ce height d'intah is average chocolate in complexion very cute tanada k'iba daidai misali, gashin tah shima curly kuma tsayin shi daidai misali atakaice dai Ummulkhair yarinya Ce mai kyaun gaske san kowa k'in wanda yarasa tasamu wadatattan tarbiya daga Iyayen tah Masha Allah, atthe age of 15 tagama secondary school d'intah, Cikin Ikon Allah taci Waec&Jamb d'intah tasamu admission at Bayero University Kano inda tah karanci Biological science, at the age of 19 tagama sch d'intah tareda saukan Al~Qur'ani mai girma, Alhamdulillah tayi service at 20yrs, tah kammala komai Lucky her! Ummulkhair tanada wani Saurayi maisuna Abubakar wanda ake kira dah Saiyadee shine Wanda takesan aure in the sense that akwai soyayya mai k'arfi atsakanin su saida kuma kash tanah fargaba sabida amatsayin tah nah 'yaamace tanah lacking lots of things daga gareshi kasancewar likita neh, she lacks his time&attention amman kuma ahakan suke soyyayar su kullum yanah batah hak'uri akan cewa watarana sailabari dah haka soyayyar su tah d'aure,

Wanene Saiyadee?
   Abubakar Saiyadee d'aaneh ga Alhaji kabeer Fahad dah Hajiya Humaira, shine d'ansu nafari saikuma k'annen sah uku wato Bilal, Amrah dah Autah Amal, Saiyadee yayi karatun sah nah likitanci a ABU Zaria sannan yadawo garin kano yayi bautan k'asa Idan cikin ikon Allah yasamu Offer nah aiki a Private clinic nah International Clinics & Maternity kano, yana cikin wannan neh Allah yakuma d'aukaka sah inda yakuma samun aiki a AKTH Kano, so sai yahad'a biyun hakan bah k'arramin tightening schedules d'insa yayi bah, Saiyadee yakasance mutum mai nutsuwa Wanda koh magana batah damesa bah, kyakkyawa neh, dogochocolate in complexion, his Smile kills😆, nutsuwar Saiyadee bah k'arramin Jan hankalin en matah yake bah, hakan yasah suke yauwan damunsa dah zancen so Masha Allah bah maikula matah baneh so one way or the other he's always avoiding ladies, acikin rashin kula matan nasah Allah yahad'a shi dah watah baiwar Allah a asibiti mai suna Ummulkhair har yakasance shine mai checking d'inta when it comes to health har takaida yazama Family doctor d'insu yasamu karbuwa awajan iyayen tah sosai sabida halayyar sah tagari, Ummulkhair dah Saiyadee sun shak'u sosai tun suna abin nasu kamar brother and sister, har suka fuskanci suna san junansu, tareda alk'awarin aure, saidai kuma atimes suna samin matsala sabidaSaiyadee is so devoted to his work itah kuma Ummulkhair tanada zafin kishi amman sabida san datake masah takan danne zuciyar tah akan wasu abubuwan dah take lacking daga gareshi, sosai take kuka wani sa'in amman sam batah ta'ba nunawa agidan su bah sabida tasan iyayen natah suna sanshi kuma sun amince dah abinda ke tsakanin su, saidai kawai idan abin yadame tah sosai takan fad'awa k'anin tah yayi matah addua Akan auran tah dah Abusaiyeed d'intah!

Tofah gawani sabon salo koya zaman auren Saiyadee dah Ummulkhair zai kasance? Kubiyoni muji nima nah ka du fah🙆..
Ku biyomu A kashi na biyu...
Share:

1 comment:

  1. A gambler places bet at the wrong sportsbook - Dr.CMD
    The 상주 출장안마 gambler who placed a bet at a 강릉 출장안마 wrong sportsbook is 구미 출장샵 in fact a gambler. According 양주 출장안마 to a survey conducted 영주 출장샵 by the

    ReplyDelete

DO MIN SAMUN IN GATTACCEN WEBSITE DANNA NAN


ciga nan domin wosu muhimman bayanai

Wikipedia

Search results

Popular Posts

Total Pageviews

Followers

choose your language

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *