This blog is created to brings for you some life stories in english language, hausa novels and latest news updates, especially on latest job in nigeria.

YAR MAHAUKACIYA KASHI NA BIYU (2)

Ta daga tarin tarikicen su take tana ihun kuka tana Kiran Mahaukaciyata ina kike ? Da kyar ta dena dage dagen ta matso kusa da jaririn nan ta tsura masa ido yaron sai kuka yake tun karfinsa wani tausayinsa ya kama ta ta Mika hanu a nitse ta dauko shi ta jawo ruwan nan ta wanke masa fuskarsa ta dorashi a bayanta ta dauki zanin nan da Larai ta bata ta goya shi ta fito ta fantsama neman Mahaukaciya ,  Wai shin wacece Yar mahaukaciya? Yarmahaukaciya ita kanta bata san sunanta ba bata san na mahaifiyarta ba , ita dai ta fara wayo ta ganta a gidansu bola kuma taji yara na kiranta da *Yar Mahaukaciya* ana kiran mahaifiyarta da *Mahaukaciya* duk da irin tarin daudar da suke ciki da cin abinci marar kyau da kwana a waje marar kyau idan ka kalesu zaka gane cewar fararen mutane ne rayuwa ce kawai ta mayar da su masu duhu , Yar Mahaukaciya ba arabi bale boko , bata da kowa sai Mahaukaciya , tarbiyarta tarbiyar Allah ce domin tanada nutsuwa tana masifar son Mahaifiyarta Mahaukaciya , bata son komai ya rabeta kulun cikin shan dukanta take domin idan ta kawo mata abu mushe taki ci sai kawai ta daneta wataran ta dura mata wataran kuwa ta samu ta gudu ,
Abincinsu gida gida take bi tayi aikace aikacen ragwayen mata ta samu abinda ta samu ta kai musu su ci abinsu kuma ruwa na kwata ne kadai basa sha domin tana yin iya kokarinta don ganin mahaukaciya ta kwana da ruwa a dakin , tun tana karama suke cikin bolar nan wataran ta wayi gari taga Mahaukaciya na dauke da ciki bata san KO na waye ba hasalima sai da taji yara na fada ta gane inda suka dosa tayi mamakin inda mahaukaciya ta samu cikin nan harma tayi tunanin KO hakan kawai ake wayar gari da shi , ita dai bata da mai bata amsa hakan yasa ta yi shiru abinta take lalaba mahaifiyarta cikin tsananin so da kauna iya labarin tarihin mahaukaciya Kenan. Tafe take da dan yaro a bayanta tana girgizashi tana fadin kayi shiru dan Mahaukaciya muje mû nemo Mahaukaciyarmu mu kawota gidan mu ta goya sabon dan mu , kayi shiru Dan mahaukaciyana tana ta yawo gaba daya ta jigata sai jiri take na tsananin yunwa ga Dan mahaukaciya sai dai ta bashi ruwa yara kuwa banda tsokanarta ba abinda suke duk inda ta zaga sai an biyota ana fadin lah Yar mahaukaciya ta sato beby har ta ISO wajen wani police zata huce taji yace " ke yar mahaukaciya dan wa kika sato haka? Tayi narai narai gabanta na mugun faduwa ta ce " Mahaukaciya ta haife shi kuma ta gudu, Ya zabga mata mari har sai da ta dan fara sakin fitsari ya damketa sai police station , suna zuwa ya Nuna cewar ta sato yaro ne suka shiga tambayarta amsar dai data ce Dan Mahaukaciya ne hakan yasa suka kunce yaron suka shiga nadarta Dole sai ta fadi inda ta sato yaro banda kuka ba abinda take suna tsaka da dukanta sai ga tsohon daraja shima police din ne aman ya fisu mukami , yana zuwa ya tambayi mai tayi, Ilyasu yayi masa bayanin ai ga abinda aka kamata da shi, Tsohon daraja ya ce "tabas kwanakin baya naga Mahaukaciya da ciki a jikinta kuma yau na ganta wajen kasuwa ba cikin sanan saninta duk jini ne tabas wanan yaro *Dan Mahaukaciya ne* dan haka ku saki baiwar Allahn nan tayi tafiyarta 
Haka suka saketa ba dan ransu ya so ba domin sun so ta kwana a nan suyi anfani da ita ,sai dai kash tsoho ya kawo cikas, Da kyar take takawa domin ta daku ta dauko dan Mahaukaciyar tayi wajen kasuwar don neman Mahaukaciya tana tafe tana kuka yaron na kuka tayi kasuwa neman duniyarnan ba Wanda bata yi ba ta juyo ta nufi wani layi tana tafe 'tana kugin sunan Mahaukaciya har ta isa wata makaranta ta zauna tayi tagumi almajirai sai shigi da fici suke suna ta sha'aninsu har akayi sallar isha'i bayan an gama sallah Malan ya fito daga masalaci ya hangi yatinyar nan zaune tana ta jijiga yaro a hanunta kawai sai wani tausayinta ya kama shi ya matso yayi mata salama, Ta dago jajayan idanuwanta masy shige da na misa ta sauke su saman fuskar wanan Malan mai cike da Haiba ta amsa salamarsa 
Ya ce " Baiwar Allah lafiya kike zaune a nan? Ga yaronki da alama yunwa yakeji to ki bashi ya sha mana Yar Mahaulaciya ta kale shi tace " Malan ai ruwan ya kare babu kuma abincinsa 
Malan sai yaji tausayinta ya ce tashi mû shiga gidana a tatsa miki nonon akuya tayi sabuwar haihuwa sai ki bashi ya sha , ta mike har tana harde kafafuwanta ta bi bayansa suka shiga gidansa, Matansa biyu dayar mai kirkin gaske DAyar kuwa tadi dafi zafi hakan yasa ya nufi dakin saratu ya fada mata ta fito ta taimaki yarinyar nan da danta,Saratu ta fito suka gaisa da yar Mahaukaciya tace miko yaron a bashi nonon akuya kema kije ga ruwan dumi kiyi wanka domin da alama sabuwar haihuwace Yar Mahaukaciya ta ce " nayi wanka? Da gaske?
Saratu ta ce " eh man ga bokici ki dauka ki zuba ruwan sai ki dan sirka da na rijiyar ki je kiyi wanka shima bara nayi masa sai a bashi nonon 
Sai washe hakora take domin itadai da wayonta har ta manta rabonta da tayi wanka ta jawo isashen ruwa ta kai bayi ta aje saratu ta bata soda ta dauko mata jacen kayanta ta mika mata har tana fadin ki wanka ruwan zafin da kyau fa saboda jego ita dai har lumshe ido take tana zuba ruwa a jikinta kafin ta fito Saratu ta wanke dan mahaukaciya ta bashi nonon akuya ya sha sosai har ya samu wani ni'imtacen baci mai dadi 

Wanka take tun karfinta wani bakin ruwa na zuba daga jikinta yana bin magudadar ruwan nan da nan sai gâta ta fara haske tamtar mai , ta cire ledar dake rufe a kanta ta dauki sodar nan ta ringa kwabata a cikin gashin kanta nan da nan naga wata irin dauda mai yauki tana zuba daga kanta ta kama kwarara ruwa gaba dayanta ta darwaye jikinta dagowar da zata yi na zaro ido domin gashin kanta ba baki bane kalar 🙍🏼 masara ne yelow gaba dayansa aman yalow mai haske ga shegen tsayi da gareshi na tambayi kaina wai Yar Mahaukaciya yar hausawa ce kuwa? Ta dauko ledarta ta daure kanta ta saka kayan da Saratu ta bata sai ajiyar zuciya take domin ta rabu da kashi 80 na daudar dake jikinta tana fitowa gaban Saratu ya fadi , duk irin kirkin saratu matsalarta daya ce kishi Allah yayi mata kishin mijinta tamkar mai , hakan yasa da Sauri ta daukowa Yar Mahaukaciya yan tsumakoron da ta dadauko mata ta bata ta hada mata da tuwon lamshi mai yawa ta ce " to yar uwa rufe gidan zamu yi kinsan Malan ba a nan yake kwana ba hakan yasa Mike rufe gida da wuri  Yar Mahaukaciya ta kama godiya harda tsugunawa saratu ta ce ba komai ta dora mata dan Mahaukaciya ta goya ta dauki sauran kayan tayi gaba tana yiwa Allah godiya taci GABA da Neman Mahaukaciya..
To ya zata Kaya? Muhadu a kashi na Uku. 

Share:

No comments:

Post a Comment

DO MIN SAMUN IN GATTACCEN WEBSITE DANNA NAN


ciga nan domin wosu muhimman bayanai

Wikipedia

Search results

Popular Posts

Total Pageviews

Followers

choose your language

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *