This blog is created to brings for you some life stories in english language, hausa novels and latest news updates, especially on latest job in nigeria.

*'YAR MAHAUKACIYA KASHI NA DAYA 1




Ko karin amai take tana jan nunfashinta , ita kuwa ta daneta ta matse mata baki ala Dole sai ta dura mata danyen misan da ta tsinto a cikin bola , MAhaukaciya ce na hango ta dane wata yar budurwa tana kokarin dura mata mushe a bakinta ita kuwa ta gumtse bakin taki budewa , tana tsaka da kokowa da ita sai naga ta dakata , ta ja da baya kuma sai naga ta saka ihu ta shiga shure shure tana dafa cikinta da alama nakuda ce ta taso mata , yarinyar nan naga ta taso da gudu tana ta bibiyar wanan mahaukaciyar tana fadin , sanu haihuwar ce ?

Ita dai Mahaukaciya ba bakin magana banda juya kai ba abinda take hakan yasa yarinyarnan fita da gudu daga cikin tsumakoran da suka saka suka dadaure sukayi dan dakinsu inda zapi , sanyi , damana ke riskarsu , tana FIta tayi ta gudu tana haki da kyar ta samu ta fito cikin layin domin a can cikin bola ne suke can karshen anguwa , tana fitowa ta tsaya tana waige waige ta rasa ina zata dosa domin neman taimako , wani gida ta hango tamkar kango ta nufa domin wani lokacin sunkan sakata kai shara gidansu wato bola , su bata dan kanzo da ruwan daurayarsu na kayan wankin su wani lokacin har barinta suke ta debi na rijiya taje su sha dadinsu ita da Mahaukaciya ,

Tana shiga ta rafka salama ta ja gefe ta rakube , wasu yara naga sun fito su kansu daudar jikinsu ta ishe su suna ta wasa suna ganin wanan yar budurwar saï naji sun fara wake suna fadin *Ke mai suna Yar Mahaukaciya yaya haukan ki Yar Mahaukaciya , shin ina babarki Mahaukaciya tana ta zuba haukan? Yar mahaukaciya* ita kuwa sai murmushi take aika musu bata ce komai ba , har suka gama daukar maganar su suka tafi abinsu , ta kusan rabin awa a tsaye sai ga uwar gidan ta fito ta sha damara da niyar yin surfe tana ganin Yar mahaukaciya tayi hamdallah ta yafitota, Yar mahaukaciya ta matsa da Sauri ta zuguna a gabanta ,
Larai ta ce " idan abinci kike so zan baki da ruwan rijiya ke harma da zanin daurawata aman sai kin surfe min wanman dawar gaba dayanta, Yar mahaukaciya ta juya inda aka nuna mata dawa ta hadiyi wani yawu mai daci ta ce " To uwar gida ran gida zan surfa yanzu kuwa?

Larai ta washe hakora ta kama mata buhun dawar suka tsayar da tirmin da tabaryar ta gyara yagegen zanin dake daure a jikinta ta shiga daka ba kakautawa , tun da rana ba ita ta gama ba sai yama lilis , Larai ta aiketa tayo mata cefane taje har cikin kasuwa a kafarta ita dai fama take ta gama ta koma wajen Mahaukaciya tasan yanzu ta dena iface ifacen domin takanyi hakan ,
Ba ita ta gama bautar gidan yawa ba sai da wajen shigar magariba , larai ta harhado mata abinci harda na shekaran jiya ya gama yin tsami ta turo mata harda kanzo ta sauye mata shi a cikin wani bokici da ya gama yin tsatsa sanan ta ce ta jawo guga biyu ta isa gudun kar ruwan rijiyar ya kare ta je ta jawo guga biyun ta sauye a tsohuwar jarkarta ta dauka gaba daya tana tafe tana Sauri yara kuwa sai binta suke suna fadin yar Mahaukaciya ita kuwa bata kulasu famarta ta isa bola Tana zuwa ta hango dan karton da ta kara ta rufe an janye shi ta kara Sauri ta shige cikin kewayen nasu , jini jini ta fara gani a dashe a ko'ina ta yaye rufar da tayi da ledodi tana yayewa gabanta na faduwa don abinda idanuwanta suka gani bata san sanda ta saki bokicin abincin da ta wuni tana aiki dalilinsa ya zube a nan ba ta dauki hanunta ta dora saman kanta saman bakar ledar da tayi dan kwali da ita ta kurma ihu domin jariri ta gani konce cikin jini yashe a nan gashi ba Mahaukaciya ba alamarta da gudu ta karasa ta shiga dage dage da alama neman Mahaukaciyar take.
 Shin ina mahaukaciya? Yaron nan wa ya haife shi? Su waye Mahaukaciya da Yar Mahaukaciya? mu hadu a kashi na biyu.


Share:

4 comments:

DO MIN SAMUN IN GATTACCEN WEBSITE DANNA NAN


ciga nan domin wosu muhimman bayanai

Wikipedia

Search results

Popular Posts

Total Pageviews

Followers

choose your language

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *