This blog is created to brings for you some life stories in english language, hausa novels and latest news updates, especially on latest job in nigeria.

HIKAYAR SHEHU JAHA KASHI NA UKU 3

DAGA ALJANNA NAKE



Wata rana Shehu Jaha ya gamu da wata mace kan hanya. Sai ta tambaye shi daga ina ya fito? Sai yace da ita daga jahannama. Da jin haka sai ta tambaye shi ko ya ga yaron ta da ya rasu a can? Sai yace da ita ya gan shi a tsaye a kofar Aljanna an hana shi shiga har sai an biya masa bashin da yake kansa. Sai matar ta bashi kudin da zasu biya wannan bashin, ta kama hanya ta tafi gida, ta bawa mijinta labarin abin da ya faru, sai nan da nan mijin nata ya zabura ya hau dokinsa don ya kamo barawon. Ko da shehu ya hango shi, sai yayi wuf ya fada wani gida da ake yin nika, yace da mai nika, don Allah ka cece ni wani Azzalumi ne ya biyo ni, saboda haka taimakon da zaka kayi mini shine ka karbi rigata ka sanya, ni kuma ka bani taka na sa, sai ka hau wannan bishiyar ka buya a cikin rassanta. Sai mai nika ya amince da wannan bukata, da mai gida ya iso gidan nika ya shiga, ya tambayi inda barawon yake, sai shehu ya nuna masa mutumin da yake kan bishiya, nan da nan sai mutumin ya cire GWADONSA ya bar dokin sa, ya hau bishiya don ya kama barawon, sai fa Shehu ya dauki gwadon ya yi maza ya dare dokin ya sheka a guje. Bayan nan sai mai doki ya dawo gida a kasa, ya ce da matarsa babu shakka mutumin nan daga lahira yake kuma can zai koma, saboda haka na ba shi mayafina da dokina na ce ya hada da kudin da kika ba shi ya kai wa yaron...hahahhhahah
Share:

No comments:

Post a Comment

DO MIN SAMUN IN GATTACCEN WEBSITE DANNA NAN


ciga nan domin wosu muhimman bayanai

Wikipedia

Search results

Popular Posts

Total Pageviews

Followers

choose your language

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *