kujerar da yake zaune. Fararen kaya ne a jikinta amma gaba daya sun
baci da jini wuyanta a yanke jini na zuba har tsartuwa yake yi. Idanunta kuwa
sunyi jawur jini na bulbula daga ciki haka hakuranta sun kara zarowa sun fito
waje jini cike da bakin. Kuma a hakan
murmushi take wani irin sauti na fita kadan-kadan.............
😰 Kodai aljana ya
zane 🙆🏻??
Muktar da gaba daya ya tsorace ya gigice
har ya fadi. A hankali ya dago kai dan kara tabbatar da abunda ya gani shin ko
gaskiya ne ko kuwa idanunsa ne kawai suka nuna mishi hakan. Abun mamaki a dagowar da yayi wayam yaga
gurin ba komai. Yana nan dai a tsaye yana tunane-tunane wannan al'amari domin
yasha kai karfe sha biyu amma tun da yake yau kusan shekara daya da bude shagon
amma ba'a taba tsorata shi ba sai yau "shin ko dai da gaske gamo
nayi" ya tambaya kansa.
Karar da ta doki dodan kunnan sa ne ya
dawo dashi daga tunanin da yake. Daga
bangaren hannunsa na dama karar Kofatu kamar duban dawaki ne suka nufo shi yaji. Nan da nan ya juya a firgice yana neman
fadawa shago. Wasu bakaken hallitu ne
wanda masu jikin doki dukan su bakake ne amma ba kai a jikinsu sune suka nufo
shi a sukwane.
Koda idanunsa sukayi tozali da wannan
mugun abu, hankalinsa ne ya dugunzuma dan tsabar tsorata a million ya fada
shago bai ko tsaya kulle shagon ba haka kuma baisan lokacin da ya tsallake
dogon bincin da ke raba masu sayayya da cikin shagon ba. A bayan bencin ya sama
wani dan lungu ya labe yana maida nunfashi day-day. Duk jikinsa karkarwa yake
idanunsa nan-da-nan suka saki ruwa. Kuka
ya farayi shabe-shabe ya fara magana a hankali cikin muryar sa dake rawa yana
fadin "Wannan wane irin bala'i ne ni kam yau na shiga uku..." Surutai ya tayi shi kadai sai da ya dau kusan
mintuna 20 a cikin shago yayi lumi ko motsin kirki baya yi kuma karar dawakin
nan har yanzu a kwaita.
Can dai yaga wannan bata yi ga zafin
dake adabarsa sai gumi yake, hakan tasa shi fitowa daga inda ya labe a hankali
ya dan leka kofar shagonsa wayan baiga komai ba sai karar da yake ji. Ya dade
nan a tsaye ko zaiji karar ya ragu amma ba alamar raguwar. Ga zafin ya fara cin
karfinsa ya fara magana cikin murya irin ta mai kuka ko gunguni. "Haba
wllh fita zanyi bazan tsaya zafi ya kashe ni a banza ba. Wallahi fati zanyi ko
me zai faru ya faru. Juyawa yayi ya dauki makulan shagon bai ko tsaya debe
kudinsa ba. Ya fara yunkurin tsallakowa
bayan ya tsallako ne ya bi a hankali kamar munahiki ya leko shagon ta
bangaren da yake jin karar.
Leka warsa keda wuya sai yaji kamar an
dauke wuta dif! Karar ta dauke. Hakan ya bashi dama da karfin gwiwa na fitowa
da sauri ya garkame kofar shagon yanufi hanyar gida da gudu-gudu sauri-sauri
takun da yayi bai wuce 15 ba sai gani yayi wutacen nan gaba daya sun dauke
dif!. Al'amarin da tasa shi yayi tsaye cik kenan. Kamar walkiya haka yaga wani
farin abu ya gifta ta gaban shi duk da duhun amma yaga abun kamar mutun lokacin
tsoro ya kara rufe shi, Suman tsaye yayi a gurin tsabar tsorata da yayi.
Sanda aka shafe kusan mintuna 10 yana
wajen a tsaye ya rufe idanu alamun haske ya gani hakan yasa ya bude idanunsa ai
kuwa sai yaga wutar ta dawo. Nan fa ya ranci ta kare ya zura a guje kamar wanda
zai tashi sama. Yana wuce wani mangwaro
yajiyo dariya a saman shi, a cikin gudun ya wai-wayo abunda ya gani ne yasa shi
har saida yayi tuntube karfin gudun yasa har sai da ya wuntsila yayi kungun
bala. Yarinyar nan ya gani kamar dazun
duj jini na fita a jikinta kuma itace ta dage kai sama tana gagaba dariya marar
dadin ji.
Bai kula da ko yaji ciwo ko baiji ba. Ya
tashi ya ruga a guje yana ihu. Bai daina
ganin yarinyar na fito mishi a sifofi na ban tsoro ba har ya kawo gida. Da
shigar sa gida ko tsayawa sa kubobin kawai banka kofar yayi. Dake yasan kyauran
mai jamlock ne.
Da gudu ya fada daki UⓂⓂEIY
ZEEY (matarsa) na kwance a kan gado tana barci.
Yabi ta kanta ya tsallaka dayan gefan tuni ya ja (blanket) bargo ya rufa duk
zafin da ake fama da shi. Nauyin sa ne ya tayar da Ummiey daga barci waigawa tayi dan ganin waye
sai ganin shi tayi ya kudun-dune cikin bargo yana sauke nunfashi day-day tayi
mamaki mutumin da baya san zafi ko kadan kullum in yazo sai ya mayar da fanka
ta bangaransa amma yau gashi ya shiga bargo lalai ba lafiya ba.
"Mai gida-Mai gida baban
HAWWER-baban HAWWER lafiya kuwa?"
Haka ta dinga jero mishi tagwayen sunaye hade da dadabarsa tana
tambayarsa. Karkarwa taga duk jikinsa ya hau yi. Domin shi kam abunda yake ji yayin da yake ji
bashi take fada ba kuma ba muryarta yake ji ba.
Domin wata murya yake ji mai abun tsoro tana fadin "Mu...ktar...m..u..ktra"
a slow muryar ke tafiya.
Ummiey ganin karkarwar da yake tayi yawa
ta dan daga murya "Baban Hawwer lafiya kuwa". Yayin da shi kuma yaji an daga mishi tsawa da
wata muryar mai razanarwa ance, "Kai muktar magana fa nake maka". Firgigit ya tashi zaune. Maimakon yaga
matarshi ummiey. Yariyar nan ya gani kamar yanda take dazun dan yanzu ma tafi
ban tsoro domin dogon gashin kanta mai-makon ya zuba a bayanta sai mikewa yayi
tsaye cir! Yayi wani irin fadi A sama. ('Kai duk wanda yayi arba da wannan
yarinya ala dole hantar cikinsa ta kada dan tsoro, In ma bai sume ba')
Muktar kuka ya farayi yana ja da
baya-baya yana bata hakuri a haka har ya surmuyo kasa daga kan gado bai ko jira
kuma ba yaci gaba da ja bayan. Ummiey na
gannin mai gidan nata ya fado daga kan gado yana kuma kallonta yana kuka ta
tabbatar da ba'a hayyacinsa yake ba. Hakan yasa ta matso daga kan gadon ta
sakko a hankali take binshi tana tambaya. "Baban hawwer wai me ke damunka
ne?, ka min magana mana".
Yayin da shi kuwa yarinyar yake gani
tana tunkaro shi hakan yasa ya kara sauri wajen jan gindin da yake yana yin
baya yana fadin. "Na shiga uku yau
naga ta kaina, dan allah kiyi hakuri karki kashe ni shin dan naki taimaka miki
shikenan nayi laifin da za'a azftar dani har haka. *DAGA TAIMAKO* dan allah karki kashe ni".
Ummiey da jin wannan kalamai na fita a
bakin mijin nata sai tayi tsaye cik! Tana kallon shi cike da mamaki tana cewa
"Lalai baban hawwer yau ba lafiya kake ba. Yanzu ni din kake cewa zan
kashe ka ni?".
Yayin da shi kuma yake jin wani abun
daban sabanin abunda take fada. Domin
shi yarinyar yaga ta tsaya tana gagaba dariya kafin ta fada da murya mai fitowa
bibiyu. "Kai muktar ka sani ka debo ruwan dafa kanka, a cikin kifayen da
kake kamowa yau ka kamo ajalin ka. Nan take yaga wata wulshe-shiyar wuka ta
bayyana a hannun yarinyar.
Ihu! Ya fara kurmawa yana fadin
"Wallahi na tuba baran kara ba, dan allah ki yafe min duk abunda kike so
zan baki. Duk lokacin da kikaji yunwa ki dinga zuwa ina baki abinci ko da kuwa
zakiyi ci Goma ne a rana amma dan allah ki taimaka kiyi min rai karki kashe
ni". Ummiey taga abun da mijin nata
yake ya fara yawa harda ihu nan ta fara tunanin ko ta leka ta kirawo makwabcin
su ne. Kuma sai dai tace bari ta karasa gare shi. Tahowa tayi cikin sauri ta mika hannunta zata
taba shi. Ihuu! Ya kurma mai razanar wa kafin ya zube kasa sumame. domin shi
yarinyar ya gani ta zo kanshi ta daga wuka zata caka mishi................
Tahowa tayi cikin sauri ta mika hannunta
zata taba shi. Ihuu! Ya kurma mai razanar wa kafin ya zube kasa sumame. domin
shi yarinyar ya gani ta zo kanshi ta daga wuka zata caka mishi» Ummiey gaba daya ta firgice kamar ta kurma
ihu! Itama. Ganin mai gidan nan nata a
kass sumame. A rude tayi waje tana zubda hawaye. Da sauri taje ta bude randar
kasar ta wacce ruwan ciki yayi sanyi sosai kamar ansa kankara tasa moda ta
kwalfo tayi cikin daki da gudu.
Tana zuwa batayi Wata-Wata ba ta kwaraya
mishi gaba dayan ruwan da ta debo. Firgi-git ya mike zaune yana nishi yana yan
waige-waige kamar wanda yake neman wani abu
dayan hannun sa kuma goge fuskarsa yake domin ruwanda Ummiey ta kwaraya
mishi. Ganin baiga abun da yake zatan gani ba yayi saurin mikewa ya nufi kofar
daki a guje ya rufe ya sakala kubobi biyu yana fadin.
"Ummiey wllh kashe ni zatayi
taimaka ki kama a jawo wardrobe din nan
a kara rufe dakin". Ummiey kam
tsaye tayi ta saki baki tana kallansa yanda duk yabi ya rikice yake abu kamar
mahaukaci. "Baban hawwer wai lafiyar ka kalau kuwa? Ya kake wasu irin
abubuwa ne haka wanda ban taba ganin kayi kwatan-kwacin kalar su
ba?".
Tsawa ya daka mata kamar yanda ya saba
dama baya jiya mata dadi, ba dan Ummiey mai hakuri ce ba da tuni ta bar masa
gidansa to amma sai akaci sa'a irin matan nan ne masu hakuri tayo gadon gidansu
dake babban ta shine limamin masalacin juma'ar anguwar kuma baban malammi ne
masani. Itama kuma haka tayi sauka har
biyu.
Zabura tayi tsawar da ya daka mata. "Nace miki kizo ki kama wannan wardrobe
din mu kai mu rufe kofar aljana ce in ta sake shigowa kashe ni zatayi".
Ummiey sai yanzu ta gane mijin nata gamo
yayi. "Baban hawwer wacce aljana kuma"?. "Oh! My god ya fada. Tunda bazaki kama
min ba baza ki taimakawa mijinki ba so kike ta halaka ni to bari in kai ni ai
zan iya". Kiki-kiki ya jawo wardrobe har kofar dakin ya danne kofar. Danne
wa keda wuya yaji an fara girgiza kofar dakin da gudu ya haye gado ya lulube.
Ummiey ce tazo kanshi ta fara tofa mishi addu'o'i har allah ya taimaka barci
yayi gaba da shi.
Tunda asuba da ya tashi yaci gaba da
zabur-zaburansa. Ummie na tofa mishi addu'a amma taga abun yafi karfita hakan
yasa ta dauki waya ta kira babanta tana kuka ta gaya mishi duk abunda ya faru.
Yace gashi nan zuwa. Mukhtar ba abunda yake
sai surutai duk bayan yan mintuna kuma sai ya dinga tsorata yana boyewa
yana fadar "gata nan gata nan".!
Ummiey ita kanta ta shiga rudani.
Ba'afi mintuna 20 ba malam hamza ya
karaso gidan koda Mukhtar ya jiyo sallamarsa da gudu ya fito ya makal-kale
malam yana surutai saida malam yayi da gaske tukun ya raba jiknsa da na Mukhtar
lokacin ya fara tofa mishi adduo'i tukun ya samu haukan da yake ya dan lafa
malam yasa shi ya zauna a tabarma da ummie ta shimfida. Bayan sun zauna ne
malam ya fara karanta ayyatul kursiyyu tare da sauran ayoyi masu karfi. Ba'a dade da fara karatun ba sai ganin wannan
yarinyar ta bayyana cikin kayan da Khadija ta saka mata. A gaban malam ta zauna hade da musu sallama.
Muktar har zai ruga malam ya zaunar da shi. Hatta ummie ta tsorata domin ganin
abun tayi kamar a mafarki.
Malam ya kalle ta yace "baiwar
allah me wannan mutumin ya miki an bani labarin irin azabtar da shi da kika yi
jiya". Muryar ta ba dadin ji tace, "ka tambaye shi malam shi ai yasan
abunda yayi". Malam baiyi gardama
ba ya juya ga muktar ya tambaye shi me ya mata. "A tsorace yac malam wallahi
ba abunda nayi mata shagona taje tana nuna alamun yunwa take ji a rana ta farko
na kore ta a rana ta biyu kuma ganin ta takura min na dake ta".
"Karya kake muna fiki azzalumi
macuci, Ko daya ba dan wannan ne na shiga rayuwarka ba. Wannan ma nayi ne dan
in tabbatar da rashin mutuncin ka da mutane ke fada sai naji kai da bakin ka ma
fada kake. Malam muktar Shin har ka manta abunda kayi shekara daya da rabi baya
da suka wuce?. Yarinyar ta fada cikin
tsiwa tana hararen shi. Nan fa kwakwalwarshi ta shiga juya mai yana kokarin
tuno wani abu. Ganin ya shiga dogon
tunani ta sake daga mishi wani tsawan wanda ita kanta ummie ta firgita kamar ta
fada daki taji. "Kaaaai! Mugu wato har ka manta yaron da ka kashe ka
rabasu da dukiyarsu ka raba yaya da kanwa. a fadama ko?". Dummm!
Gaban muktar ya fadi jin ta tado zancen da a tunaninsa
ba wanda ya san
shi daga allah sai shi sai kuma wannan
yarinyar. (What!) "Yaron da ya kashe?". Ummiey da malam ne suka fadi hakan a tare.
Bugun kirjinsa ne ya tsananta nan take
jikinsa ya fara bari. Motsowa ya farayi gaban Yarinyar yana fadar "Dama ke
aljana ce ban sani ba. Don allah ki rufa min asiri karki tona wannan sirrin duk
abunda kike so zanyi amma ki taimake ni
karki tona wannan sirrin...."
Tsawar da ta daka mishi ce ta tsayar da shi nan take ta wani bata rai
fuska ba wal-wala. "Bani bace domin dani ce da bazaka kwana ba a ranar. Ka
basu labarin abunda ka aikata wa wannan yarinyar da kanka, in kuwa ba haka ba
yanzu ka gayawa yan garin ku". Ta karashe maganar cikin daga murya. Nan
take tsoran Mukhtar ya karu. "To-to bari in fada amma dan allah karki min
komai".
Malam da diyarsa ba abunda suke sai
kallo da sauraren ikon allah. Ummiey tunani take shin wannan wane BOYAYYEN
AL'AMARI ne? Wanda bata sani ba game da mijinta. Ita dai bayan mugun halin sa
da kowa yasan da shi bata kuma san da wani ba. Mukhtar ganin kowa yayi shiru
shi ake saurare ga kuma wannan aljanar da ke mishi wani mugun kallo mai
tsoratarwa. Ya shiga basu labari..............................
MU HADU A KASHI NA GABA....
No comments:
Post a Comment