This blog is created to brings for you some life stories in english language, hausa novels and latest news updates, especially on latest job in nigeria.

MATAR DR. SAYYEEDI KASHI NA BIYU 2


Bayan Ummulkhair tah tashi daga gajeren baccin daya kwashe tah wayan tah neh first thing data fara dubawa aikuwa taga har lokacin babu missed calls d'in Saiyadee koh kad'an, batayi mamaki bah dan sunsaba irin haka dashi hakan yasah tah murgud'a baki tasoma game abinta, kiran Mummyn tah taji tuni tah tashi batare dah k'ara 'bata lokaci bah dan amsa kiran Mummyn natah, parlour tafara dubawa batah ganta bah hakan yasah tanufi d'akin tah, sallama tayi kamun tace Mummy gani nazo, "toh khairat shigo manah, cikin nutsuwa tahmurd'a k'ofan tashige ciki murmushi tasakar wa Mummyn natah, sannan tace Mummy ganinan, kallon tah mahaifiyar tatah tayi cike dah so sannan tace khairat yau bazamu ci abinci baneh koh laifi mukayi neh, naga bakya zancen dinner neh, laa Mummy laifin meh? bakumin komai bah Wallahi kinga game nake awaya nah duk nah sha'afa bara naje nad'aura, "Mummy meza adafa toh, murmushi Mummy tayi sannan tace waida cewa nayi funkaso dah miyar gyad'a koh? naga Abbanku yanaso, tam Mummy bara nakwaba saina had'a miyan, Mummy nah flour koh wheat? Kiyi mixing both er albarka, tam shikenan Mummy nawuce kitchen idan Affan yadawo kice masa ina kitchen, murmushi kawai Mummy tayi,
tuni Ummulkhair tawuce kitchen tahwanke hannun tah sannan tah kwa'ba flour+wheat d'in tabarshi yatashi batare dah wani 'batah lokaci bah tafara had'a miyan Fans bakuji k'amshi ya gauraye groups bah, ai Ummulkhair badaga nanba when it comes to cooking, phone d'intah dake kan freezer neh yasoma ringing dubawa tayi taga MyHalf, dasauri tayi picking tasaka akunne murmushi tasoma yi saikuma tayi shuru batace komai,
Ummunah....
Shuru batah amsa bah,
Ummunah koh fushi kike dani neh?
Sai asannan tace, "uhm uhm bah fushi nake bah,
toh kiyi hak'uri aiki neh yayi min yauwa kema kinsan yanayin aikin namu koh,
Uhm nasani Allah yataimaka, yak'ara d'aukaka,Ameen Ummunah mekike yi?
Girki nakeyi!
Hmmm kice yau su Mummy zasuci jagwalgwalo,
hmmm bawani nan, dad'i dai,
ahh toh mutum da iyakar sah abinda ya iya dafa ruwan zafi inashi ina wani girki,
dariya tah kyalkyale masah harda rufe fuska kamar yanah gabanta, shuru yayi yanah sauraran dariyar tah mai sakashi farin cikin gaske kaunarta yanah ratsa shi tun daga kai har k'afa, Ummunah yace muryan sah k'asa~k'asa,
Na'am Ya Saiyadee, tah amsa cikin murmushi,
I miss U, yace
I miss U more ai tafad'a kamar maisan yin kuka,
bawani nan injiwa, nafi missing d'inki kinaganin koh aiki nakasa yi sosai sabida banji muryan ki bah,
hhhh toh naji nikam kaga harna gamayin miya fah,
Ai miyan bazata yi dad'i bah tunda bakiji murya nabah kika yishi
Laa injiwa toh?
Injini mijin Ummulkhair
dariya tayi sannan tace "hakadai kace ya saiyadee amman dah dad'i
toh Ummunah mezakiyi yanzu?
Funkaso zan soya shi kadai yarage min,
toh bara nazo nataya ki karki k'onamin hannun,
chab saikace yarinya ai kona k'one ni macece,
toh kajisu su matah, maza suja gefe
dariya tasaki sosai tace Ya Saiyadee nibance bah,toh naji Ummunah bara nacigaba dah aikinah anjima zan sato hanya nazo naduba ki, kiyi ahankali kada ki k'one kinji pls,
toh Saiyadeen Ummu, Insha Allah!
Mezan siyo miki?
Bkomai tah amsa,
Kin tabbatar babu abinda kikeso,
Eh babu deary,
Toh shikenan later deary bye!
Uhm kawai tace kamar tayi kuka sam bataji dad'in yankewar wayan bah saidah tad'au kunsan 30mins azaune kafin tah dauki funkaso wanda daman yatashi tasoma zuba shi cikin mai, tanayi tanah tunanin Saiyadeen tah gaba d'aya jitayi hankalin tah yakasa kwanciya sotake yau taganshi sun dad'e basu had'u bah sabida yanayin aikin sah,Wayartah tah d'auko tamishi message kamar haka,
 Salam Abusaiyeed Dan Allah yau kazo I badly want to see U kagafa U promised, pls stick to your promises dear, I miss U tekia!
Ajiye wayan tayi tacigaba dah abinda takeyi bayan tagama tazuba komai cikin warmers tayi setting table, d'akin Mummy tawuce straight idan tah sheda matah cewar tah kammala komai hartayi musu ginger drink, sosai Mummy taji dad'i tah dinga matah Addu'oi dah shimata albarka, dariya tayi kana tace bakomai Mummynah hakk'inah neh nah taimaka miki ai, Mummy Dan Allah Ya Saiyadee yace zaizo nan bada jimawa bah,
toh shikenan maraba d'an Albarka maza kije ki k'imsa kafin yazo, Allahu yaAlbarkaci rayuwar Ku baki d'aya!
Ameen tace tah mik'e cike dah farin ciki hartakai bakin k'ofar d'akin tah watah zuciyar tace matah, hmmm sai wani murna kike kamar kin tabbatar dazuwan nashi saikinzo kinyi kwalliyar ki abanza ma baizoba kodai bah Saiyadee bah kinmanta aikin shi yafiye masa komai arayuwa, take taji mood d'inta yacanza tayi deciding taje tad'au phone d'intah tacigaba dah game d'intah kawai bayan tayi wanka,
 On reaching to her phone taga hanging message from MyHalf, murna cikin Ummulkhair ba amagana tuni tah manta dah dukkanin damuwan tah tanah bud'ewa taga reply kamar haka
 "Insha Allah Ummunah dah anyi magrib kafin Isha'i zaki ganni nima I also miss U, sonake naganki heartbeat! Tsalle tayi dan murna tuni tayi hanyar fita adaidai k'ofa tah tarar dah Affan tsaye yanah kallon tah yanah dariya kamun yace, "Sis kawo muraba kyautar kud'in dakika samu dake sakaki murna haka!
Toh masu karatu,yau kuma anan zamu dasa aya sai kuma gobe in Allah yakai mu ,mu hadu a kashi na uku..
Domin Karin bayani ko shawara zaku iya tuntuban Admin na WhatsApp namu " Haidar" ta wannan layi :08100806588.. Ku huta lafiya..
Share:

No comments:

Post a Comment

DO MIN SAMUN IN GATTACCEN WEBSITE DANNA NAN


ciga nan domin wosu muhimman bayanai

Wikipedia

Search results

Popular Posts

Total Pageviews

Followers

choose your language

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *